Kamfanin zirga-zirgar jiragen saman Kenya Airways ya gabatar a ranar Lahadi da wani sabon jadawalin tashin jirage domin rage tsaikon mutanen da suke jibge a birnin Nairobi tun bayan gobarar da ta lakume wani bangaren karbar baki na filin jiragen sama a ranar Laraba da ta gabata. Shugaban dake kula da harkokin kamfanin, mista Mbuvi Ngunze ya bayyana cewa, an samu jiragen sama da za su tashi daga birnin Nairobi a ranar Lahadi zuwa wasu yankuna talatin da hudu.
Mista Ngunze ya nuna cewa, gyara wani bangaren dake kula da karbar baki da kuma kafa na'urorin bincike zai taimaka wajen karbar bakin dake wucewa.
Gobarar da ta abku ranar Laraba ta lalata falon karbar baki na babban filin jiragen kasa da kasa na Nairobi. A ranar Jumma'a, shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya ba da sanarwar cewa, gwamnatinsa ta dauki niyyar sake gina wani sabon sashin zuwan baki da fitarsu na wucin gadi, da zai fara aiki nan da 'yan makonni masu zuwa.
Haka kuma shugaba Kenyatta ya nuna fatansa na ganin taminal na hudu da ake cikin ginawa a filin jirgin zai iyar fara aiki kafin lokacin ya kamata a kammala ginin, a farkon watan Maris na shekarar 2014.
Hukumomin kasar Kenya sun dauki niyyar sabunta bangarorin karbar baki da fitarsu na daya, na biyu da na uku, da bayan an kammala gina taminal din wucin gadi na wannan filin saukar jiragen sama. (Maman Ada)