in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya ta yi kira a cimma wata jituwa domin samun zaman lafiya a Somaliya
2013-08-07 12:12:27 cri

Gwamnatin kasar Kenya ta yi kira a ranar Talata ga dukkan bangarori masu ruwa da tsaki da su sake gina kasar Somaliya ta hanyar yin shawarwari, hadin kai da kuma girmama juna domin kauce wa gurgunta zaman lafiyar da bai dore ba a cikin wannan kasa dake kusurwar nahiyar Afrika. Babbar sakatariyar tsaro, madam Monica Juma ta bayyana a yayin wani taron manema labarai da aka shirya a birnin Nairobi cewa, kasar Kenya na goyon bayan hanyar gaba daya da take taimakawa kowa da samar da wani yanayi da 'yan kasar suka gabatar da kansu domin hada kan 'yan kasa da kawo zaman lafiya a kasar Somaliya.

'Muna nuna goyon baya ga tsarin dake tabbatar da hanyar cimma muhimman batutuwan kawo zaman lafiya mai dorewa a kasar Somaliya, kawar da kungiyar Al-shabaab da kuma ayyukan ta'addanci a cikin wannan kasa.' in ji madam Juma, jakadiyar kasar Kenya dake kasar Habasha. 'Wadannan batutuwa na bukatar yin shawarwari da cimma ra'ayi guda tsakanin bangarori daban daban da wannan batu ya shafa kai tsaye game da rikicin kasar Somaliya.' in ji madam Juma.

Jami'ar ta yi wadannan kalamai kwanaki biyu bayan manyan shugabannin shiyyoyin kasashen Afrika dake taimakawa tawagar tabbatar da zaman lafiya ta Afrika dake kasar Somaliya (AMISON) suka bayyana cewa, zargin da ba shi da tushe da korafe korafe da ake wa wasu mambobinsu ya kamata a daina.

Shugabannin shiyyoyin sun bayyana ra'ayinsu, bayan wasu kafofin kasar Somaliya da Kenya suka rawaito kalaman wasu shugabannin kasar Somaliya dake bukatar kasar Kenya ta janye sojojinta daga kasar Somaliya. Amma daga baya, tawagar kasar Somaliya ta janye wannan sanarwa a yayin wani zaman taro da aka kammala a kasar Uganda, bayan kasar Kenya da wasu kasashen shiyyar suka nuna adawa kan wannan sanarwa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China