Ibrahim Boubarca Keita ya samu lashe zaben shugaban kasar da aka kammala a kasar Mali, inda ya kada abokin hamayyarsa Soumaila Cisse wanda nan take shi kuma ya amince da hakan a cikin wata sanarwa taya murna da ya aika ma zababben shugaban a Bamako, babban birnin kasar, duk da cewar ba a fitar da sakamakon a hukumance ba.
A lokacin wani taro da ya kira a gidansa tare da Ibrahim Boubarca Keita, Mr. Cisse ya sanar cewa, a shirye yake ya taimaka ma IBK wajen cimma aniyarsa da yake da shi na son cigaban kasar a matsayinsa na sabon shugaba.
Sai dai kuma sakamakon da aka fitar a ranar Lahadi ba a kai ga sanarwa a hukumance ba, ya sa magoya bayan Soumaila Cisse korafin cewa, an tabka magudi wanda shi ya hana sahihancin sakamakon da za'a fitar a hukumance nan gaba wani daraja. (Fatimah)