Madam Espinoza ta ce, ya zuwa yanzu kungiyar EU ta tura masu sa ido fiye da 100 ga kasar Mali, wadandan za su sa ido kan dukkan ayyukan zaben shugaban kasar da odar yin zaben a manyan yankuna 5 na kasar kamar Segou, Kayes, Mopti da dai sauransu.
Kafin wannan, hukumar zaben kasar Mali mai zaman kanta ta bayyana cewa, tawagar masu sa ido dake kunshe da membobi fiye da dubu 5 daga kasar da sauran kasashen duniya ta dauki nauyin sa ido ga zaben shugaban kasar. Yawancin masu sa ido daga kasar Mali sun zo ne daga wasu kungiyoyi da hukumomi masu zaman kansu a kasar. Kana yawancin masu sa ido na kasa da kasa sun zo daga kungiyar AU, EU, kawancen kasashe masu amfani da harshen Faransanci, ECOWAS da dai sauransu. (Zainab)