in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dan takarar shugaban kasar Mali ya nuna kyamarsa ga magudin zabe
2013-08-10 15:55:44 cri

A yammacin ranar Juma'a 9 ga wata, dan takarar kujerar shugaban kasar Mali, Soumaila Cisse ya nuna kyamarsa ga magudin zabe, wanda aka yi ran 28 ga watan Yulin da ya wuce, inda ya sha alwashin lashe zagaye na biyu na zaben, wanda za'a yi gobe Lahadi.

A yayin hira da kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua, lokacin da yake karkare yakin neman zabe Cisse ya ce, wasu kura-kurai da aka samu sun kawo rashin inganci zagayen farko na zaben domin an samu wadannan matsaloli tsakanin 'yan takara da kuma yadda aka tafi da shirin.

A zagayen farko, dan takarar mai shekaru 68 kuma tsohon framinsitan kasar kana shugaban jamiyyar Rally For Mali (RPM) Ibrahim Boubakar Keita ya samu kashi 39.79 cikin dari na yawan kuri'u, inda ya zarce Cisse wanda tsohon ministan kudi ne na Mali, inda shi kuma ya samu kashi 19.7 cikin dari.

Tun da babu dan takara da ya samu kuri'u mafi yawa yadda aka tsara, an shirya yin sabon zagayen zabe ran Lahadi.

Dan takarar mai shekaru 63 ya ce, ya gano cibiyoyin jefa kuri'a na karya, kuma an ga kuri'u da aka jefa masa an watsar a tituna, inda ya lura cewa gwamnati ce ke dauke da nauyin tabbatar da tsaro da sa ido kan zaben.

A halin da ake ciki, Cisse yace rabin 'yan kasar Mali ne suka jefa kuri'a a takin farko inda ya nuna fatan a samu canji a zagaye na biyu.

Ya ci gaba da cewa, yana da kyakkyawar fata a zagayen na biyu, inda ya ce yana mai burin samun kuri'a daga wajen mata da matasa.(Lami Ali)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China