Mista Liu Guijin, wanda a baya shi ne manzon musamman na gwamnatin Sin mai kula da harkokin Afirka, ya ce, a yayin babban zaben, masu sa ido na kasar Sin sun duba yadda aka jefa kuri'a a tashoshin jefa kuri'u fiye da 60 da ke larduna 5 na kasar. A ganinsu, an samu nasarar gudanar da babban zaben a kasar.
Liu Guijin ya kara da cewa, tawagar sa ido ta kasar Sin ta yi na'am da amincewar da takwarorinta na kungiyar tarayyar Afirka wato AU da kungiyar SADC suka nuna kan babban zaben Zimbabwe, kana ta yi kira ga jam'iyyu daban daban da suka shiga zaben da su amince da sakamakon zaben, kuma ya kamata wadanda ba su amince da sakamakon ba su daidaita sabani bisa tanadin dokoki cikin ruwan sanyi, a maimakon yin amfani da karfin tuwo.(Tasallah)