Wannan dai sanarwar ta nuna cewa, shugaban mai ci zai samu damar sake ci gaba da mulkin kasar ta Zimbabwe, har izuwa wasu shekaru 5 nan gaba.
Sai dai duk da karbuwar da sakamakon zaben ya samu daga magoya bayan jam'iyyar Zanu-PF mai mulki, a hannu guda tsohon babban dan adawar shugaba Mugabe, kuma firaministan kasar Morgan Tsvangirai ya yi watsi da sakamakon, yana mai cewa, za su dauki matakan kalubalantar abin da ya kira sakamakon mai cike da magudi a gaban kotu. Bugu da kari Tsavangirai ya ce, shi da jam'iyyarsa ta MDC-T ba za su taba shiga gwamnatin da za a kafa karkashin jam'iyyar Zanu-PF ta shugaba Mugabe ba.(Saminu)