in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Lionel Andres Messi:babban jagoran kungiyar Barcelona
2013-08-10 16:28:04 cri

Wannan sakamako ya sheda cewa Messi wanda ke kan gaba wajen cin kwallo ya samu maki 80, yayin da dan wasan dake matsayi na 2 ya samu 11 kawai, wato bambanci yana da yawa.

Ganin yadda kungiyar Barcelona ke dogaro ga Lionel Messi ya sa ake tunanin cewa, idan Messi bai halarci wasa ba, ko kuma ya gaza nuna kwarewa sosai a wani wasa, to, me zai faru ga kungiyar Barcelona? Tarihin kungiyar ya sheda cewa, a gasar Cin kofin zakarun turai da ya gudana a kakar wasanni ta shekarar 2012 zuwa ta 2013, FC Barcelona ta fuskanci matsala yayin wasan ta da AC Milan, inda aka tashi da ci 2 da babu. A wannan wasan, Messi ya taba kwallo da kafansa sau daya kacal a da'irar dake kusa da ragar kungiyar AC Milan, kuma ko kadan bai yi barazana ga abokan karawa ba.

A wasan kusa da na karshe na gasar Cin kofin zakarun turai, Barcelona ta kara da Bayern Munich karo 2, inda a karon farko, Messi ya kasa nuna kwarewarsa sakamakon rauni da ya samu a kafa, don haka Bayern ta lashe Barcelona da ci 4 da nema. Sa'an nan a karo na 2, Bayern ta lashe Barcelona da ci 3 da nema, kasancewar Messi ba ya jin dadi, bai ma shiga wasan ba, kuma rasa Messi da kulaf din ya yi, ya sa kungiya ta rasa karfinta.

A kugiyar Barcelona, Messi shi ne dan wasa mafi muhimmanci, a yayin da kulof din ke ci gaba da kokari samarwa Messi muhalli mai kyau don faranta masa rai. Bayan kammala wasan cin kofin zakarun turai, na kakar wasanni ta shekarar 2010 zuwa ta 2011, Guardiola, mai horar da 'yan wasan Barcelona, ya bayyana wata manufa da ake wa lakabi da 'akidar Messi', wato ya kamata kungiyar ta shigo da 'yan wasa masu dacewa, don tallafawa Lionel Messi, ta yadda zai samu jin dadin taka kwallo. Idan Messi ya kasa nuna kwarewa, to zai zama domin kulob din bai ba shi muhalli mai kyau ba ne.

Manufar da Guardiola ya dauka ta sanya 'yan wasan kungiyar su ma sun fara amincewa da akidar Messi. David Villa Sánchez, wanda ake ganin ba ya shiri da Messi, shi ma ya kasakantar da kai, yana mai cewa Messi tutarsu ce, don haka dole ne a sanya shi farin ciki da jin dadi, ganin hakan zai amfanar da kungiyar Barcelona baki daya. Ya ce zai yi kokarin tarayya da Messi a fagen sarrafa kwallo don faranta masa rai.

Ban da haka kuma, Guardiola ya yada wannan manufa ga kungiyar kasar Argentina. A lokacin da Alejandro Sabella, mai horar da 'yan wasan kungiyar Argentina, ya tambayi Guardiola kan dabararsa wajen yin amfani da Lionel Messi, inda Guardiola ya amsa da cewa, ba bukata a yi magana mai yawa don gane da Messi,illa dai a sanya sauran 'yan wasa su kewaye shi don rage matsalar da zai fuskanta. Ya kamata, a cewar Guardiola, a dinga sauraron ra'ayin Messi, don sanya shi ganin muhimmancin da yake da shi, sa'an nan a amince da Messi, ba kuma tare da matsa masa lamba sosai ba.

A takaice, hakan ne ke sanya Messi jin dadi da farin ciki. Wannan manufa ta yi amfani a kungiyar Argentina, ganin yadda Messi ya ci kwallaye 12 ga kungiyar a shekarar 2012, jimillar da ta yi daidai da bajintar da Gabriel Batistuta ya kafa a tarihin kungiyar ta Argentina.

Wannan matsayi na fice da Lionel Messi ya samu, tilas ne yayi tasiri ga sauran 'yan wasan kungiyar ta Barcelona, amma ko an amince, ko kuwa a'a, tilas ne a bi wannan tsari da kungiyar ta dauka.

A matsayinsa na jagoran kungiyar Barcelona, Messi ya kan yi fada ga abokan wasansa idan suka yi kuskure. Ga misali, a watan Maris na shekarar 2012, kungiyar Barcelona ta yi kunnen doki marsa ci da AC Milan, a gasar cin kofin zakarun turai ta UEFA, a wannan wasa Messi ya nuna fushin sa ga Cristian Tello, wanda ya hana shi wata kwallo, da ya buga da kansa, ta kuma kaucewa raga. Sai dai Cristian Tello yana da hazaka, domin mako guda bayan lamarin, Barcelona ta lashe Sevilla da ci 2 da 1, inda Tello dake bangaren hagu ya samu kwallon da Messi ya ba shi, nan take ya sake mika kwallon a gaban raga ga Messi, inda kuma nan take Messin ya jefa ta a raga, lamarin da ya farantawa Messi ransa matuka.

Amma fa ba dukkannin 'yan wasa kulaf din na Barca ne ke jituwa da Messi ba, wasunsu na da kwarewa sosai, sai dai basa samun damar nuna hakan, sakamakon kasancewar Messi dake da muhimmanci a idanun masu horar da 'yan wasan kulaf din fiye da su. 'Yan wasa irinsu Zlatan Ibrahimovic, David Villa Sanchez, da Carlos Alberto Tévez, na fuskantar kalubale sosai sakamakon haka.

Wasu manazarta harkokin wasan kwallon kafa dai na ganin ko sauran 'yan wasa na so ko a'a, Lionel Messi zai ci gaba da kasancewa ginshikin kulaf din Barcelona. A duk loakcin da aka tuna Barcelona a nan gaba, tilas ne a ambaci gudummawar da wannan shahararren dan wasa ya baiwa kulaf din. (Bello Wang/Saminu Alhassan Usman)


1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China