in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Andy Murray ya kafa tarihin lashe gasar Wimbledon, bayan kasarsa ta Birtaniya ta sha jiran samun wannan nasara a tsahon shekaru 77
2013-07-13 20:43:49 cri
Dan wasan kwallon tanis daga kasar Birtaniya Andy Murry ya hucewa kasarsa takaicin kasa daukar kofin Wimbledon tsahon shekaru 77 da suka gabata, bayan da a bana ya doke kwararren dan wasan tanis din nan Novak Djokovic daga kasar Sabiya, a wasan karshe da suka buga ranar Lahadin data gabata. Fafatawa tsakanin wadannan 'yan wasa ta kawo karshe ne bayan shafe awanni 3 da mintuna 9 ana dauki-ba-dadi, inda aka kammala wasannin karshe da maki 6 da 4, da 7 da 5, da kuma 6 da 4.

Masu bibiyar harkokin wasanni sun ce kasar ta Birtaniya ta dauki wannan kofi ne a karon karshe tun shekarar 1936, lokacinda dan wasan kasar Fred Perry ya samu nasarar lashe gasar wancan lokaci. Kammala wasan karshe na wasan ranar Lahadin data gabata ya jefa farin ciki zukatan masu kallon wasan na tanis, inda shi kuwa Murry dan shekaru 22 da haihuwa ya yi jifa da abin wasa dake hannunsa, da hular da take kansa, ya kuma yi ihu, kafin ya durkusa kasa ya rufe fuskarsa da tafukan hannayensa.

"Wannan wasa shi ne mafi tsanani da na taba bugawa a tarihin wasana, lashe gasar Wimbledon wani abu ne da har yanzu nake mamakin faruwarsa. A karshen wannan gasa na kidime, bamma san abin da ke faruwa ba, kawai dai na shiga wani irin yanayi na daban" A kalaman Murray, bayan samun nasarar da ya yi ta daukar kofin duniya ajin kwararru na wasan na tanis.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China