Wata majiya daga rundunar sojin kasar ta tabbatar da sace ma'aikatan zaben a garin Tessalit dake Arewacin kasar, yayin da suke tsaka da gudanar da ayyukan share fagen babban zaben dake tafe.
Kawo wannan lokaci dai maharan basu fidda sakon dalilin yin awon gaba, da wadannan ma'aikata ba, kuma babu wata kungiya data dauki alhakin gudanarda hakan.(Saminu Alhassan Usman)