in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu na MDD ta amince da cigaban ayyukan ofishin wanzar da zaman lafiya a Burundi
2013-02-14 16:34:20 cri
Kwamitin sulhu na MDD a jiya laraba 13 ga wata ta amince da kudurin cigaba da ayyukan ofishin wanzar da zaman lafiya a Burundi har na tsawon wani shekara daya.,wato zuwa 12 ga watan Fabrarirun na 2014.

Kwamitin mai wakilan kasashe 15 sun amince da hakan ne bisa la'akari da cigaban da aka samu a Burundi wanda ya hada da mikar da tsarin dokoki na kasar,kare 'yancin dan adam tare da ci gaban tattalin arziki na mata da matasa da kuma al'ummomin da tashin hankali ya rutsa da su.

Inganta hukumomin zai zama wani babban kafa ga samun nasarar,inji kwamitin, lokacin da mambobin ta suka bada goyon bayan kara azama akan ayyukan da zasu samar da cigaba a fannin siyasa,tattalin arziki da kuma shugabancin gwamnati da zummar kafa wata tushe mai karfi da za'a samu dawwamammen walwala da kuma tattalin arziki.

Haka kuma kwamitin ya yi kira ga gwamnatin kasar Burundi da ta yi kokarin kiran babban zaben da zai kunshi kowa a ciki a shekara ta 2015 ta hanyar cigaba da tattaunawa tsakanin dukkan masu ruwa da tsaki da suka hada da kungiyoyin masu zaman kansu domin bada tabbacin samar da kafa ga dukkan jam'iyun siyasa. (Fatimah Inuwa Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China