Babbar kotun duniya dake Haque na kasar Netherlands za ta saurari karar mataimakin shugaban kasar Kenya William Ruto game da taka hakkin bil adama a ranar 10 ga watan Satumba.
A cikin wata sanarwar da kotun ta fitar a jiya Litinin, ta ce, alkalai sun yanke shawarar fara sauraron karar a yanzu maimakon lokacin da aka ware a da domin ba da lokaci ga wanda aka kara ya shirya dalilansa.
Ana bukatar sabon shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta da mataimakinsa William Ruto da su bayyana a gaban kotun domin amsa laifuffukan da ake zargin su da su na taka hakkin bil adama a lokacin babban zaben da aka yi a kasar a tsakanin shekarar 2007 da ta 2008, inda mutane fiye da 1,100 suka mutu a tashe-tashen hankulan da suka biyo baya, zargin da dukkannin shugabannin suka musanta.
Shugabannin kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU a lokacin taron cika shekaru 50 na kungiyar da aka yi a kwanann nan a birnin Adiss Ababa na kasar Habasha sun nuna kin amincewarsu da tsoma bakin kotun duniya a cikin al'amuran kasar Kenya.
A cikin wata wasikar da aka aike wa babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon, shugabannin kungiyar sun yi nuni da cewa, wani tashin hankalin na iya barkewa idan har aka ce, za'a gurfanar da shugabannin a gaban kotun.
Haka kuma, mai kare William Ruto ya bukaci a saurari karar ne a kasar da ke gabashin Afrika a maimakon cibiyar kotun duniyar dake Haque. (Fatimah)