in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A Najeriya an gargadi wasu jihohi 14 kan yiwuwar aukuwar ambaliyar ruwa
2013-07-30 21:02:48 cri
Ma'aikatar kula da muhalli ta Najeriya ta sanar a ranar Litinin 29 ga wata a birnin Abuja cewa, akwai yiwuwar ruwan saman da za'a yi kamar da bakin kwarya a wasu jihohin kasar guda 14, daga ranar 30 ga watan Yuli zuwa ta 6 ga watan Agusta, zai iya haifar da bala'in ambaliyar ruwa mai tsanani.

Cikin wata sanarwar da aka fitar, an ce, jihohin da lamarin ka iya shafa sun hada da, Benue, da Kebbi, da Gombe, da Zamfara, da Yobe, da kuma Jigawa. Ragowar sun hada da Borno, da Katsina, da Bauchi, da Kano, Sokoto, Kaduna, Taraba da kuma jihar Adamawa. Hasashen dai ya nuna cewa, za'a fuskanci bala'in ambaliyar ruwa a birane da garuruwa da dama dake wadannan jihohi.

Ma'aikatar kula da muhalli ta Najeriyar ta yi kira ga hukumomi, gami da al'umomin wadannan jihohi 14, da su yi hattara, su kuma dauki duk wani matakin da ya wajaba, wajen kaucewa hasarar rayuwa da dukiyoyi.

Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China