Akalla sojan kasar Sudan guda ne ya rasu, baya ga wasu biyu da suka jikkata, sakamakon wani dauki-ba-dadi da ya auku tsakanin dakarun sojin kasar ta Sudan SAF, da takwarorinsu na Sudan ta Kudu a Tashween dake yankin Heglig mai arzikin man fetir.
Wata sanarwa da kakakin rundunar sojin kasar Sudan Sawarmy Khalid Saad ya fitar, ta bayyana cewa, fadan ya barke ne, bayan da sojin Sudan ta Kudu suka kutsa kai cikin yankin Tashween dake karkashin ikon Sudan da yammacin ranar Litinin, lamarin da ya nan take ya haifar da musayar wuta tsakanin bangarorin biyu. An ce, jim kadan da aukuwar wannan lamari, jagororin rundunonin biyu sun shiga tsakani kuma al'amura sun daidaita.
Dakarun bangarorin biyu dai sun sha kaiwa junansu hari a wannan yanki na Heglig, tun bayan da sojin Sudan ta Kudu suka samu nasarar kwace shi ran 10 ga watan Afirilun shekarar bara, yayin da kuma dakarun Sudan suka sake kwace shi kwanaki 20 bayan aukuwar hakan.
Kawo yanzu dai, kasashen biyu sun gaza raba iyakar da ta hada su, suna kuma ci gaba da mahawara kan batun mallakar yankuna 5 dake kan iyakokin nasu, ciki hadda yankin Abyei dake fama da tashe-tashen hankula. Har ila yau musayar wuta da sojin bangarorin biyu suka yi na nuni ga halin rashin tabbas da shirin warware takaddamar da kasashen biyu ke yi cikin lumana. (Saminu)