130731bagwai
|
Yayin da al`ummar musulmin duniya suka shiga zangon karshe na wata azumin Ramadan, a yanzu haka daukacin musulmin duniya sun dukufa wajen tabbatar da ganin sun samu dacewa da ganin daren lailatul kadr, dare mafi mahimmanci a jerin daren dake cikin watan Ramadan.
A duk lokaci irin wannan musulmi na mayar da hankali sosai wajen gudanar da ibadoji domin samun amincewar Ubangiji Madaukakin Sarki.
Duk dacewa dai ana son musulmi ya kasance mai bayar da himma wajen gudanar da ibada a lokacin watan Ramadana ganin irin darajar da watan ke da shi a tsakanin watanni musulunci, amma ana kwadaitawa duk wani musulmi irin alherin dake tattare da kwanakin karshe na watan Azumi.
Malam Muhammad Nazifi Inuwa babban malami ne a jihar Kano ya yi man karin bayani game da wannan dare da kuma falalar dake cikinsa.
Malamin ya ce daren lailatul Kadr dare ne mafi daukaka a tsakanin jerin daren dubu, a don haka ne Manzo Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kadaitawa musulmi cewa su lalubi wannan dare a tsakanin 21 ga watan Ramadan ko 23 ko 25 ko kuma 29.
Malam Muhammad Nazifi Inuwa ya ce an bayar da wannan zabi ne domin musulmi ya kara zabura sosai.
To sai kuma wani batun na daban wanda ya shafi al`adar Hausawa kuma suke gudanar da shi a tsakiyar watan azumi.
Tashe wani wasa ne na kayatarwa wanda Hausawa ke yi idan azumi ya cika kwana goma.
Akasari ana shafe kwanaki goma ne ana wannan wasa na tashe wanda ya kunshi maza da mata, yara da manya, to amma wani lokaci a kan shi ga goman karshe na Azumi ana gudanar da wanann wasa na Tashe.
Shi dai wannan wasa na tashe yana zuwa ne a sigogi daban daban, wani lokaci ana gudanar da shi cikin tsarin barkwanci, wani lokaci kuma a kan yi shi a tsarin wa`azantarwa, kuma sau tari a kan rinka sanya kida da waka cikin raha.
Dr. Ibrahim Garba Satatima Malami ne a sashen koyar da harsunan Najeriya na Jami`ar Bayero, ya yi man karin haske gami da asalin tashe da kuma matsayin sa a jerin al`adun Hausawa.
Ya ce an fara wannan wasa ne sama da shekaru 500 da suka gabata, kuma Kalmar tashe ta samo asali daga Tashi.
Dr. Ibrahim Garba Satatima ya ce Hausawa na amfani da wannan dama ce wajen tashin jama`a lokacin sahur, al`adar da har yanzun nan Hausawa ke yinta.
Daktan ya ci gaba da cewa ta fuskar kiwon lafiya Tashe na taimakawa sosai, bayan musulmi sun sha ruwa, su kan yi amfani da wanann dama wajen motsa jikinsu kafin kwanciyar barci, koda yake ba sai da daddare ake gudanar da tashe ba. Ana yinsa ko da rana ne ko kuma da maraice.
Babban fatan duk wani musulmi dai a nan shi ne dacewa da rahamar Allah a koda yaushe. (Garba Abdullahi Bagwai)