in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya sabunta takunkumin da ya kakabawa Liberia
2012-12-13 09:54:23 cri

Cikin wani kudurin da daukacin mambobin kwamitin tsaro na MDD 15 suka amince da shi, kwamitin ya amince da ci gaban haramcin samun izinin fita zuwa kasashen ketare, ga rukunin 'yan kasar Liberia, da aka yi imanin suna yiwa shirin tabbatar da zaman lafiyar kasar kafar ungulu, tare kuma da haramta shigar da makamai cikin kasar.

Wannan sabon kuduri da ya tanadi tsawaita wa'adin takunkumin da aka kakabawa wancan rukuni na 'yan kasar Liberia, ya kuma bai wa masu sa ido da kwamitin ya tanada, damar ci gaba da aikinsu na lura da aiwatar da takunkumin. Bugu da kari, an bukaci tawagar 'yan sa idon da ta hada gwiwa da gwamnatin kasar mai ci, da ma wani rukuni na kwararru daga kasar Cote d'Ivoire, domin aiwatar da wasu ayyukan nazarin yadda wannan takunkumi ke aiki, a cikin kasar da ma kasashen dake makwaftaka da ita, domin fidda rahoto mai kunshe da sakamakon aikin nasu, da ma dukkanin wani batu mai alaka da karya ka'idojin da aka gindaya. Har ila yau, kwamitin tsaron ya ce, kasar Liberia na da zarafin neman a sake kwaskwarima ga wannan kuduri kafin cikar karin wa'adin da aka yi, muddin dai ta kai ga cimma ka'idojin da aka gindaya.

Takunkumin da kwamitin tsaron na MDD ya sanyawa kasar ta Liberia shekaru kimanin 10 kawo yau dai, ya biyo bayan dinbin matsalolin masu alaka da yakin basasa da yaki ci yaki cinyewa a kasar, baya ga haramcaccen cinikin makamai da lu'u lu'u, da bangarorin 'yan kasar ke ci gaba da yi, kawo wannan lokaci.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China