A ranar Alhamis ne ma'aikatar kula da harkokin tsaron jama'a ta kasar Sin ta bayyana cewa, kasar Sin za ta tura rukunin 'yan sandan kwantar da tarzoma domin su hade da tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD da ke Liberia.
Wannan shi ne karo na farko da kasar Sin ta aika 'yan sandan kwantar da tarzoma zuwa Afirka. A cewar wata sanarwar da ma'aikatar ta bayar, kasar ta Sin za ta tura wadannan 'yan sandan kwantar da tarzoma zuwa kasar Liberia ne a watan Satumba.
Su dai wadannan 'yan sandan kwantar da tarzoma da kasar Sin za ta tura kasar ta Liberia, an tsamo su ne daga cikin rukunin jami'an 'yan sanda da ke lardin Heilongjiang na arewa maso gabashin kasar Sin, bayan da suka ci jarrabawar da MDD ta shirya a ranar 7 ga watan Yuli, inda suka shafe watanni 3 suna samun horo na musamman.
Tun a shekara ta 2000 ne kasar Sin ta tura jami'an 'yan sanda 1,789 domin su yi aiki a cikin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD. (Ibrahim)