in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Magatakardan MDD ya yi kiran zabe cikin gaskiya da lumana a Mali
2013-07-27 16:07:34 cri

A ranar Juma'a 26 ga wata, magatakardan MDD Ban Ki-Moon ya yi kiran tabbatar da gabatar da zaben shugaban kasar Mali cikin lumana da kuma gaskiya.

A fadin wata sanarwa da ta fito daga mai magana da yawun magatakardan, Mr. Ban ya nanata kiran tabbatar da gudanar da zaben wanda za'a yi a kasar ta nahiyar Afirka ranar Lahadi mai zuwa, cikin lumana da adalci bisa burin 'yan kasar Mali.

Magatakardan ya yi kira ga dukkan jam'iyyu da su tabbatar sun tafi da kansu cikin natsuwa, ya kuma bukaci daukacin 'yan kasar su fito su jefa kuri'a. Ya jadadda bukatar maido da odar dokokin kasa da kuma mai da hankali kan shawarwari da sulhu a kasar Mali.

Ana daukar zaben shugaban kasar Mali wanda za'a yi ranar 28 ga watan Yuli da muhimmanci wajen maido da ikon kasa da kiyaye doka bayan juyin mulkin soja da aka fuskanta ranar 22 ga watan Mayun 2012 wanda ya yi sanadin mamaya da 'yan tawaye dake da alaka da Al-Qaida suka yi a arewacin Mali.

To amma bisa goyon bayan kasar Faransa da wasu kasashe dake yankin, gwamnatin ta Mali ta yi nasarar fatatakar 'yan tawayen daga manyan birane a arewacin kasar tun cikin watan Janairu.(Lami Ali)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China