in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Tunisia na shirin kaddamar da wata cibiyar karbar matan aure da ake gallazawa ko cin zarafinsu
2012-06-21 11:39:57 cri
Kasar Tunisia na shirin kaddamar da wata cibiyar karbar matan auren da ake gallazawa ko cin zarafinsu a birnin Tunis, in ji ministar matan kasar Tunisia madam Sihem Badi.

Ministar ta bayyana hakan a yayin bude zaman taron kwararru na ranakun 20 da 12 ga watan Yuni kan " nauyin gwamnati wajen kawar da cin zafarin da ake wa mata" a kasashen Larabawa da kuma arewacin nahiyar Afrika.

Sakamakon da za'a samu kan wannan cibiya a matsayin gwaji, zai samu bazuwa a dukkan yankunan wadannan kasashe in ji madam Badi.

Ministar ta ce, abubuwan koyi da aka gabatar da kuma matakan kwararru, sun bayyana cewa wannan taro na yanzu zai taimaka wajen shirya wata dabarar kasa ta yaki da cin zarafin da ake wa mata.

Bisa kiran mai gabatar da rahoto ta musammun ta MDD game da cin zarafin mata, madam Rashida Manjo, tare da taimakon babbar hukumar kare 'yancin dan adam dake birnin Tunis, wannan zaman taro na cikin tsarin shawarwari na shiyyar kan wannan take kuma za'a gudanar da turuka biyu irin wannan a tsakiyar Afrika da kuma gabashin nahiyar.

(Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China