Idan dai ana iya tunawa, a ran 6 ga wata ne aka kashe shugaban kungiyar adawa mafi girma , kuma babban sakataren jam'iyyar dinke kasa da dimokuradiyya Chokri Belaid, lamarin da ya jawo barkewar rikicin siyasa mai tsanani a kasar.
Bayan aukuwar wannan lamari, yunkurin da tsohon firaministan kasar Hamadi Jebali ya yi na samar da daidaito ta yin kwaskwarima ga gwamnatin kasar ya ci tura, wanda hakan ya tilasta shi yin murabus daga mukaminsa a ran 19 ga wata. Daga nan ne aka nada tsohon ministan harkokin gidan kasar Ali Laarayedh, domin ya kafa wata sabuwar gwamanti.
A kuma wani taron manema labaru da aka gudanar ranar Talata Ali Laarayedh ya bayyana cewa, mutane hudun da ake tsare da su, mambobi ne na wata kungiyar masu tsattsaurancin ra'ayin addini, wadanda shekarun su suka kama daga 26 zuwa 34 da haihuwa, wasu kuwa da ma an taba kama su da aikata laifi. (Amina)