A cewar ma'aikatar shari'ar kasar babu wata doka da ta kayyade tsahon lokacin da mutum zai shafe a filin jirgin sama, yana jiran samun izinin barin kasar. A nata bangare hukumar lura da harkokin shige da ficen kasar ta ce Snowden na iya kasancewa a filin jirgin har tsahon rabin shekara, zuwa lokacin da za a tantance matsayinsa a shari'ance. Shugaban hukumar lura da harkokin shige da ficen kasar Vladimir Volokh, ya ce tun da Snowen na fuskantar barazanar tsafkewa daga Amurka, ya fi dacewa ya ci gaba da zama a filin jirgi maimakon sansanin 'yan gudun hijira.
A ranar Alhamis din da ta gabata ma dai sai da jakadan Amurka dake birnin Moscow ya sake jaddada bukatar kasarsa ta neman Rashan ta mika mata Snowden maimakon fidda shi daga kasar, sai dai tuni mai magana da yawun shugaban kasar Rashan Dmitry Peskov ya ce Rasha ba ta da niyyar mika Snowden din ga Amurka. (Saminu Alhassan)