in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Watakila Snowden ya nemi iznin zama dan kasar Rasha
2013-07-18 09:58:50 cri
Lauyan tsohon ma'aikacin leken asiri na kasar Amurka Edward Snowden ya bayyana ranar laraba cewa watakila Snowden zai nemi izinin zama 'dan kasar Rasha kuma baya so ya bar kasar ta Rasha har sai ya samu izinin samun mafaka ta wucin gadi.

Lauyan kasar Rasha dake yiwa Snowden tallafi a fuskar shari'a Anatoli Kucherena ya ci gaba da cewa tsohon mai leken asirin a takure yake .

A fadin lauyan, kasar Amurka ta daga hankalinta matuka kan yadda abubuwa suka kasance a yanzu dangane da wannan batu.

A ranar talatar nan kasar Amurka ta nemi a kori Snowden a kuma tisa keyarsa zuwa Amurka don fuskantar tuhuma da ake masa.

A fadar Kucherena, kasar Rasha bata da wata yarjejeniya da kasar Amurka dangane da tisa keyar mutane don haka Rasha bata da damar tisa keyar Snowden zuwa kasar Amurka tunda bai aikata wani abu da ya saba dokar kasar Rasha ba.

A halin da ake ciki, Kucherena yace Snowden bai cancanci samun kariya ta kasa ba.

A ranar laraba shugaba Vladimir Putin ya baiyana cewar duk wani mataki na Snowden da ka iya lalata dangantaka tsakanin Amurka da Rasha ba za'a amince da shi ba.

Putin ya ci gaba da cewa dangantaka dake tsakanin Amurka da Rasha ta fi kowace irin matsala ta leken asiri.(Lami Ali Mohammed)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China