A sa'i daya, Amurka ta ci gaba da matsa lamba ga Rasha, da fatan za a tisa keyar wannan tsohon ma'aikacin leken asiri na Amurka da ake tuhumarsa da aikata laifin leken asiri, zuwa Amurka, domin yanke masa hukunci.
A yammacin ranar 12 ga wata da misalin karfe 5, bisa agogon wurin, Snowden ya gana da memban majalisar wakilan Rasha, Vyacheslav Nikonov, da babban wakilin hakkin bil'adam na Rasha, Aleksandr Lukin, da wakilan kungiyar hakkin bil'adam na duniya, da kuma wasu lauyoyi a filin jirgin saman Sheremetyevo dake birnin Moscow.
Daga bisani, Vyacheslav Nikonov ya bayyana wa 'yan jarida a filin jirgin saman cewa, Snowden zai bukaci Rasha da ta ba shi mafakar siyasa a hukunce, kuma ya amince da sharadin da Rasha ta fitar, wato ba zai ci gaba da kawo illa ga moriyar Amurka ba.
Nikonov ya kara da cewa, Snowden ya san sharadin Rasha, kuma ya amince da shi, kuma shi ma ba ya son ci gaba da yin illa ga moriyar Amurka, sabo da yana son Amurka. Yanzu Snowden yana cikin koshin lafiya.
Game da bukatar Snowden kuma, a wannan rana sakataren yada labaru na shugaban kasar Rasha, Dmitry Peskov ya furta cewa, kawo yanzu, fadar Kremlin ba ta samu bukatar neman samun mafakar siyasa ta Snowden ba, kuma Rasha ba za ta canza sharadinta na ba shi mafakar siyasa ba.
Game da wannan batu, a wannan rana, kakakin fadar shugaban kasar Amurka, Jay Carney ya bayyana a gun taron 'yan jarida cewa, Amurka ba za ta canza matsayinta kan batun Snowden ba, inda ta riga ta bukaci Rasha da wasu sauran kasashe da su mayar da shi zuwa Amurka. (Fatima)