A wannan rana da safe, kafofin yada labaru na Rasha sun bayyana cewa, mai yiwuwa ne, Snowden zai iya barin babban filin jirgin sama na Sheremetyevo, bayan ya samu kwararriyar shaida daga hukumar kula da shige da fice ta Rasha, don shiga cikin kasar. A wannan rana da yamma kuma, bayan da shahararren lauya da ke taimakawa Snowden Anatoly kucherena ya gana da shi, ya fada wa kafofin yada labaru cewa, har yanzu, hukumar kula da shige da ficen jama'ar Rasha ba ta mika takardar shaida da abin ya shafa ga Snowden ba tukuna, sabo da haka, Snowden ba zai bar filin jirgin saman ba.
Game da wannan batu, a wannan rana, kakakin fadar White House ta Amurka Jay Carney ya bayyana cewa, yanzu, Amurka tana bukatar Rasha da ta bayyana karara game da halin da Snowden ke ciki da kuma sauyin da zai iya samu. Carney ya sake nanata cewa, Amurka ba ta canja matsayinta ba, kuma tana da isassun dokoki da cikakkun shaidu da za a mayar da Snowden ga Amurka.
A wannan rana kuma, kakakin ma'aikatar kula da harkokin wajen Amurka Jennifer Psaki ta ce, sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya riga ya aika da sako ga takwaransa na kasar Rasha Sergei Lavrov, don sake bukatar Rasha da ta ki amincewa da shigar Snowden kasar, da mayar da shi ga Amurka, don gurfanar da shi gaban kuliya. (Bako)