in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A kalla mutane 45 suka mutu sakamakon fashewar boma bomai a Pakistan
2013-03-04 14:51:09 cri

Ya zuwa ranar 4 yau Litinin ga wata da sassafe, rahotonni sun nuna cewa, a kalla mutane 45 suka rasa rayukansu, yayin da 150 suka jikkata, a sanadiyyar fashewar boma bomai a garin Karachi da ke kudancin kasar Pakistan ran 3 ga wata da dare.

Wadannan boma boman sun tashi ne a wata unguwar dake birnin Karachi a ranar 3 ga wata da misalin karfe 7 na dare bisa agogon wurin tare da lalata gine-gine biyu, kuma akwai zaton cewa, ba za'a rasa mutane da dama dake cikin wadannan gine-gine.

Har yanzu babu wata kungiyar da ta sanar da daukan alhakin kai wannan hari. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China