Kungiyar nan ta masu dauke da makamai mai suna "Harkatul Jihad aI-Islami" ta tabbatar a ranar Asabar cewa, an kashe shugabanta ILyas Kashmiri a wani harin kundin balan da Amurka ta kai a yankin Waziristan da ke arewa maso yammacin kasar Pakistan a ranar Jum'ma da dare.
Shafin Urdu na BBC ya ba da rahoto tun farko cewa, IIyas Kashmiri daya daga cikin masu dauke da makaman da Pakistan da Amurka ke nema ruwa a jallo, yana daga cikin wadanda aka kashe a harin da Amurkan da kai ta sama.
Mai magana da yawon kungiyar mai suna Abu Hanzala ya tabbatar da mutuwar Kashimiri, mutumin da ya jagoranci mummunan harin da aka kai a tashar jiragen saman sojojin ruwa da ke Karachi a watan da ya gabata, wanda ya yi sanadiyar mutuwar sojojin ruwan Pakistan 10.
Kashimiri yana daga cikin 'yan ta'adda biyar din da ake nema ruwa a jallo wadanda sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton da mikawa pakistan sunayen su a yayin ziyar da ta kawo Islamabad a watan da ya wuce(Ibrahim)