A wannan rana, bayan da majalisar dokokin Pakistan ta saurari rahoton da babban jami'in soji na kasar ya gabatar, ta yi Allah wadai da aikin soji da Amurkawa suka yi, kuma ta yi nuni da cewa, daukar matakai bisa radin kanta da Amurka ta yi ba zai amfanawa yunkurin yaki da ta'addanci a kasashen duniya ba, haka kuma ta bukaci gwamnatin Pakistan da ta kafa wani kwamitin mai zaman kansa don bincike kan wannan lamari, don magance sake abkuwar irinsa.
A sa'i daya kuma, majalisar dokokin Pakistan ta bukaci Amurka da ta dakatar da yin amfani da jiragen sama marasa matuka don kai hare-hare a kasar. Haka kuma, a cikin kudurin, an ce, ba za a amincewa sojojin kundumbala na Amurka su kai hare-hare ga yankin Abbottabad da yin amfani da jiragen sama marasa matuka don kai hare-hare a Pakistan yadda ta ga dama ba, idan kasar Amurka ba ta dakatar da daukar matakai irin wadannan ba tamkar haka, gwamnatin Pakistan za ta yi la'akari da daukar kwararan matakai, cikinsu, har da hana taimakawa kungiyar tsaro ta NATO don kai kayayyaki zuwa Afghnistan.(Bako)