in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin 'yan gudun hijirar Najeriya dake tsallakawa janhuriyar Niger ya haura 6000
2013-07-07 20:47:34 cri
Yawan 'yan gudun hijirar dake tsallakawa kasar Niger daga jihar Borno ta Arewa maso Gabashin Najeriya ya kai a kalla mutum 6,240.

Babban sakataren lardin Diffa a janhuriyar Nijar Hassan Ardo ne ya bayyana hakan, yayin zantawarsa da mataimakin gwamnan jihar Borno Zannah Mustapha, wanda ya kai ziyarar aiki a yankin. A cewarsa hakan ya biyo bayan dauki ba dadin dake wakana lokaci bayan lokaci ne tsakanin 'yan kungiyar nan ta Boko Haram da kuma jami'an tsaro a jihar ta Borno, dake Arewa maso Gabashin Najeriya, wadda kuma ke iyaka da janhuriyar ta Nijar. Ardo ya kara da cewa a kwana-kwanan nan ma sai da karamar hukumar Bosso dake Diffan ta karbi 'yan Najeriya kimanin 1,500, wadanda tashe-tashen hankula suka raba da gidajensu.

Da yake maida jawabi mataimakin gwamnan jihar ta Borno, cewa ya ziyarci wannan yanki ne domin rokon 'yan gudun hijirar su koma garuruwansu, duba da cewa tuni aka dauki dukkanin matakan da suka dace domin kare rayukansu, tare da kare sake afkuwar dalilan da suka raba su da gida.

Wata matashiya mai suna Kaka Fanta, ta bayyana yadda acewarta 'yan uwanta suka tsere, yayin wani artabu da magoya bayan kungiyar Boko Haram suka yi da jami'an tsaro. Ta ce tun zuwansu karamar hukumar ta Bosso, al'umma da mahukunta ke iyakacin kokarinsu don ganin sun kyautata musu, tare da samar musu ababen da suka wajaba, musamman ma ruwan sha.(Saminu Alhassan Usman)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China