Umar wanda ya bayyana hakan ranar Asabar 27 ga wata a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja, yayin kaddamar da sansanin zabar 'yan wasan, ya ce cikin 'yan wasa 30 da aka gayyata daga sassan kasar daban daban, 'yan wasa 8 ne kacal za su samu damar shiga tawagar da za ta wakilci kasar. A cewarsa, baya ga batun buga wa Najeriya wannan gasar dake tafe, 'yan wasan za kuma su kasance cikin shirin hukumar ta NBBF, na samar da fitattu, kuma gogaggun 'yan wasa, a yunkurin da ake yi na zakulo 'yan wasa masu basira da kwazo.
Har ila yau Umar ya bayyana kyakkyawan fatansa ga kafuwar kungiyar wasan kwando, wadda za ta taka muhimmiyar rawa, ta kuma zamo abar alfaharin Niajeriya ta hanyar lashe gasanni a nan gaba. (Saminu Alhassan)