Sanarwar ta ce, Marzouki ya yanke wannan shawara ce, bisa shawarwarin da hukumomin tsaro da sojojin kasar suka bayar, kuma bayan da ya yi shawarwari da firaministan kasar da shugaban majalisar dokoki wanda ke kula da harkokin tsara kundin tsarin mulkin kasar. A wannan rana, ministan kula da harkokin cikin gida na kasar Ali Laarayedh ya yi jawabi cewa, gwamnatin kasar za ta shirya manyan tsare-tsare wajen harkokin tsaro, addini da ilmi, kana da al'adu, don magance laifuffukan da masu tsattsauran ra'ayin addini ke aikatawa
An dai kafa doka ta baci a kasar Tunisiya ne, tun daga ranar 14 ga watan Janairu na shekarar 2011, kafin tsohon shugaban kasar Ben Ali ya bar kasar, kuma aka tsawaita ta sau da dama. Kafofin yada labaru na kasar sun bayyana cewa, dalilin da ya sa shugaban kasar na yanzu wato Marzouki ya sake yanke shawarar tsawaita wa'adin dokar ta baci a kasar, na da alaka da tsanantar yanayin da ake ciki dangane da tsaro a kasar.(Bako)