Wannan kundi ya rataya bisa damar dake tafiya da manufar cigaban al'umma zuwa wasu sabbin kalubale da suka shafi musammun ma matsalar banbance banbance dake kamari tsakanin al'ummomi da kuma yawan barazana da muhalli ke fuskanta.
Wakiliyar dindindin ta kungiyar PNUD dake kasar Togo, Madam Khadiata Lo N'diaye ta bayyana cewa wannan sakamakon bincike ya maida hankali ga adalci da karko bisa muhimmancin yin kira ga kasashen duniya kan manufofin siyasar da ake aiwatarwa da mulki nagari a duniya.
"hakan ya sami asali ne bisa yin la'akari da cewa samun bunkasuwa ba ya nufin jin dadin al'ummomi daga ribar da cigaba ya janyo" ta kara fadi.
Gabatar da wannan sakamakon bincike ya zo a daidai lokacin da kundin farko na dabarun kawar da talauci na (DSRP) ya zo karshensa wanda kuma tuni ake fara tattaunawa bisa manyan matakan da suka shafi kundi na biyu na shekarar 2012 zuwa ta 2013.
A halin yanzu bunkasuwar tattalin arzikin kasar Togo na kewaye da kashi 4 cikin 100, a yayin da kaso 61.7 na al'ummar kasar kusan miliyan 6 suke fama da talauci.(Maman Ada)