in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutum 1 ya rasu, 14 sun samu rauni sakamakon arangama tsakanin 'yan Salafist da 'yan sanda a Tunisia
2013-05-20 09:53:46 cri

Kamfanin dillancin labaran kasar Tunisia TAP ya ba da rahoton cewa, an kashe wani mai zanga-zanga ranar Lahadi yayin arangama tsakanin 'yan sanda da 'yan kungiyar Salafist masu tsatsauran ra'ayi, wacce aka hana ta gudanar da taronta.

Rahoton ya ci gaba da cewar, mai zanga-zangar, 'dan shekaru 27, na cikin masu zanga-zanga na kungiyar Salafist ta Ansar El Shariaa, inda ya samu raunin bindiga, kana daga bisani ya rasu a asibiti a yammacin Tunis.

A kalla 'yan sanda 11 da 'yan kungiyar Aalafist 3 su ma sun samu rauni, in ji gidan rediyon Mosaique.

An yi fito na fito ranar Lahadi da safe tsakanin 'yan kungiyar Salafsit da 'yan sanda a Ettadhamen, yayin da 'yan kungiyar ke kokarin yin wani taro. Yayin da 'yan sanda suka yi amfani da barkonon tsohuwa don tarwatsa taron, sai hakan ya fusata 'yan kungiyar, suka fara jifan 'yan sanda da duwatsu.

An kuma samu rahoton irin wannan arangama a garin Kairouan dake arewacin kasar.

Kungiyar ta Ansar El shariaa wacce shugabanta ya tsere, an hana ta gudanar da taro a Kairouan.

A 'yan kwanakin nan, 'yan kungiyar Salafist suna kalubalantar tsaro a kasar Tunisia, inda suke neman kafa shari'ar musulunci a kasar.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China