Karfafawa da kuma fadada huldar hadin gwiwa tsakanin Niamey da Tunisia sun kasance muhimman batutuwan zaman taro karo na 7 na kwamitin hadin gwiwar dangantaka tsakanin kasar Nijar da kasar Tunisia dake gudana a birnin Niamey tun ranar Laraba, a karkashin jagorancin ministan harkokin wajen Nijar, Mohamed Bazoum tare da takwaransa na kasar Tunisia, mista Rafik Abdessalem.
Kasashen Nijar da Tunisa na ciyar da huldar abokantaka da hadin gwiwa cikin dogon lokaci, musammun ma tun bayan da kasashen biyu suka samu 'yancin kansu a shekarar 1962.
Minista Mohamed Bazoum ya tunatar da cewa, kasar Tunisia ta kasance a sahun gaba wajen taimakwa kasar Nijar zama mambar kungiyar MDD.
Haka kuma kasar Tunisia za ta tallafawa kasar Nijar wajen farfado da tsarin bankin kasar na farko da wanda ya kasance wani ginshikin zuba jari ga samun cigaba, wato bankin BDRN, in ji Mohamed Bazoum.
Makasudin wannan taro karo na 7 na wannan babban kwamitin hadin gwiwar da aka yi bayan an gudanar da wani taron kwararrun kasashen biyu a kwanaki biyu kafin taron, shi ne na tantance sabbin hanyoyin hadin gwiwar da za'a bi tsakanin shekarar 2012 da shekarar 2014.
Kuma batutuwan dake janyo hankali a wannan karo sun shafi fannoni daban daban na dangantakar kasashen biyu kamar tattalin arziki, kasuwanci, makamashi, ma'adinai, noma, sufuri, kiwon lafiya, gine-gine, wasannin motsa jiki, kyautata zaman rayuwar al'umma, binciken kimiyya da horo.
A yayin da yake tabo maganar rashin tsaro a shiyyar, mista Bazoum ya nuna cewa, 'Ya zama wajibi mu hada karfinmu da kayayyakin aiki domin yaki da wannan babbar annoba ta ta'addanci da manyan laifuffuka dake dakushe cigaban kasashenmu da kuma kawo kalubale ga neman kyautata zaman rayuwar al'ummomin kasashenmu'. (Maman Ada)