in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Italiya ta tabbatar da kisan 'yan kasashe waje 7 da aka sace a Nigeria
2013-03-11 10:12:50 cri

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Italiya, ta tabbatar da kashe 'yan kasashen wajen nan su 7, da 'yan kungiyar kaifin kishin Islama nan ta Ansaru ta sace ranar 16 ga watan da ya gabata a jihar Bauchin Nigeria. Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Italiya ta fitar, ta tabbatar da hakan ranar Lahadi 10 ga watan nan, tana mai cewa, mutanen da aka hallaka sun hada da 'yan Lebanon 4, da 'dan Birtaniya 1, da 'dan Girka guda 1, da kuma 'dan kasar Italiya guda 1.

Sanarwar ta kara da cewa, kisan mutanen wani mumunan aiki ne na ta'addanci, wanda kasar Italiya ta yi matukar Allah wadai da shi. Daga nan sai sanarwar ta musanta kalaman kungiyar ta Ansaru, dake cewa, an kashe mutanen 7 ne, kafin, ko bayan wani dauki ba dadi tsakanin 'yan kungiyar, da kuma dakarun hadin gwiwar sojojin Birtaniya da na Nigeria.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China