Cibiyar ta kuma bayyana cewa, ma'aikatan lafiya sun yi bincike kan wadanda suka kamu da murar, inda aka tabbatar da jimillar mutane 450 na dauke da mura mai nau'in H1N1. Sakamakon haka, cibiyar ta yi kira ga jama'ar kasa, da su yi allurar rigakafi don hana yaduwar cutar ba tare da bata lokaci ba. A sa'i daya kuma, cibiyar ta bayyanawa jama'ar kasar cewa, su kwantar da hankalinsu, domin cutar H1N1 ta riga ta bulla a kasar tun tsawon shekaru 3 zuwa 4, kuma galibin mutanen kasa sun riga sun samu kwayoyin halitta na kandagarki ga illar da kwayoyin cutar ke haddasawa. (Maryam)