Taron MDD kan cinikayya da bunkasa (UNCTAD) cikin wani rahoto da ya bayar ranar Alhamis ya yi nuni cewa, ya dace gwamnatoti a Afirka su dauki matakan bunkasa sassa masu zaman kansu, in ko ba haka ba karuwar harkar cinikayya a yankuna zai amfani kamfanoni na kasashen waje ne kadai.
Rahoton bunkasar tattalin arziki a Afirka na shekarar 2013 ya lura da matakan da shugabannin Afirka suka dauka a watan Janairun shekarar 2012, na kawar da dukkan shingaye dangane da harkar cinikayya a nahiyar don bunkasa cinikayya tsakanin yankuna.
Harkar cinikaya a tsakanin kasashen Afirka ya ragu wato daga kashi 22.4 a shekarar 1997, zuwa kashi 11. 3 a shekarar 2011. Rahoton ya ci gaba da cewa, tsakanin shekarar 2007 zuwa ta 2011, harkar fitar da kaya waje tsakanin shiyyoyi a Afirka baki daya kashi 11 ne cikin dari, yayin da a nahiyar Asiya ya kai kashi 50 cikin dari, kana a kasashen Turai ya kai kashi 70 cikin dari.
Ya yi nuni da cewar, za'a fi samun amfani na gajeren lokaci a harkar cinikaya tsakanin shiyoyyi a Afirka a fuskar noma, to amma babbar moriya da kalubale kuma ta dogon lokaci za'a samu ne a fuskar bunkasa masana'antu saboda samar da kayayyaki na kawo karuwar bukata.
Rahoton da aka yi wa taken 'harkar cinikayya tsakanin sassa a Afirka, bullo da amfani dake akwai a sassa masu zaman kansu' na mai nuni da cewa, rage shingaye a harkar cinikayya tsakanin yankuna ba zai cimma buri ba, muddin ba'a samu bunkasa ba a yunkurin habaka tattalin arziki. (Lami)