in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara kafa wata masana'antar sarrafa takin zamani mai dauke da sinadarin potassium mafi girma a nahiyar Afirka
2013-07-18 16:30:05 cri
Rahotanni daga kasar Congo-Brazzaville na cewa an fara kafa wata masana'antar sarrafa takin zamani mai dauke da sinadarin potassium mafi girma a kasar a hukunce, masana'antar da wani kamfanin kasar Sin ya zuba galibin jarinta.

Aikin wanda aka kaddamar da shi a garin Pointe-Noire Montgomery dake kudu maso yammacin kasar, kuma kamfanin ma'adinai na Macquarie daga kasar Canada mallakar kamfanin ChunHe na kasar Sin. ya zuba jarin da ya haura dallar Amurka biliyan 1.3 ga kamfanin,

Gwamnatocin Sin da Congo-Brazzaville sun nuna matukar goyon baya ga wannan shiri, inda har gwamnatin kasar Congon ta baiwa kamfanin gatanci ta fannonin harajin kudin shiga da kuma kudin kwastan. Har ila yau ana fatan aikin zai samar da guraben aikin yi da yawansu ya kai mutum dubu 1 ga mazaunan wurin, matakin da zai raya tattalin arzikin kasar ta fannoni da dama.

Bugu da kari, bisa shirin da aka yi, masana'antar za ta fara aiki a karshen shekarar 2015, inda ake fatan za ta samar da takin da ya kai ton miliyan 1.2 a kowace shekara, tare da samun kudin shiga sama da dallar Amurka miliyan dari 5 a kowace shekara. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China