in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan kula da harkokin zabe na Mali ya ba da tabtancin shirya zaben shugaban kasa na ranar 28 ga watan Yuli mai zuwa cikin adalci
2013-07-25 10:31:39 cri
Ministan hukumonin kasa da gyare-gyaren kasa na kasar Mali, ta bakin magatakardan ma'aikatarsa dokta Brahima Fomba ya jagoranci wani zaman taron fadakarwa a ranar Laraba a birnin Bamako kan adalcin zabe da kuma gabatar da rahoto kan yin hadin gwiwa da hukumar tsara shiri kan bunkasuwa ta Majalisar Dinkin Duniya (PNUD). A lokacin da yake magana kan muhimmancin samun yarda daga dukkan masu ruwa da tsaki dake cikin shirye-shiryen zaben, musammun ma jam'iyyun siyasa kan sahihancin zabe, zaman taro ya kasance wata babbar dama ga manyan jami'ai daban daban na wannan ma'aikata da aka bai wa nauyin shirya zaben da suka gabatar da kasidu kan halin da ake ciki da kuma matakan tabbatar da adalci, har ma da matakan da suka shafi dokokin duba da ba da sakamakon zaben shugaban kasar da za a shirya a kasar Mali.

Haka zalika da sunan minista Moussa Sinko Coulibaly, dokta Fomba ya nuna cewa, wannan zaman taro na da manufar tattaunawa kan wasu batutuwan dake janyo hankali masu nasaba da shirye-shiryen zaben, ta yadda za a iyar kawo karin hasken da ya dace da zai taimaka wajen kwantar da hankalin dukkan masu ruwa da tsaki, musammun ma jam'iyyun siyasa kan sahihancin zaben shugaban kasa na ranar 28 ga watan Yuli mai zuwa a cikin kasar ta Mali. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China