Shugaban na Faransa ya bayyana hakan ne bayan ganawa da sabon shugaban kungiyar 'yan adawar kasar ta Syria Ahmad Jarba, inda ya ce, Faransa za ta goyi bayan gamayyar kungiyar, kuma tana shirya daukar matakan samar da tallafin jin kai da na siyasa don bai wa jama'a goyon baya.
Ya ce, kokarin da gamayyar kasashen Turai ke yi na cimma matsaya guda game da sanya wa kasar takunkumi zai hana magoya bayan shugaba Bashar al-Assad na Syria samun makamai.
A cewar hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD, yakin na Syria da aka kwashe sama da shekaru biyu ana yinsa ya halaka kimanin mutane 100,000 tare da tilasta wa mutane miliyan 1.8 kaura zuwa kasashe makwabta.(Ibrahim)