Hakan ya biyo bayan rahoton kwamitin da dan majalissar Albert Sam-Tsokwa yake jagoranta ya gabatar wanda kuma ya samu goyon baya mai rinjaye a jiya Laraba. A cewar Sam-Tsokwa, gyaran da fadar shugaban kasar ke son a yi ya yi yawa kuma ba ya da tabbaci.
A ranar 14 ga wata ne dai Shugaba Jonathan ya aika da bukatar son yin gyara na karin naira triliyon 4.9 ga kasafin kudin wannan shekarar ga majalissar dokokin kasar domin dubawa.
A cikin takardar bukatar, dan majalissar ya ce, takardar ba ta da wani shaida da zai tabbatar da ingancinta, in ban da doguwar taken bukatar, takardar ba ta da wani muhimmanci da zai nuna bukatar yin gyara ga kasafin kudin na bana, kuma takardar ba ta nuna dai dai bangaren da take son yin gyaran ba.
Kakakin majalissar dokokin Zakari Mohammed ya ce, yadda bukatar ta nuna a wasikar sai ya yi kamar tun da farko majalissar ba ta rigaya ta amince da kasafin kudin ba can baya.
A cewarsa, gyara na nufin akwai dokar da take da rauni, amma a yanayin gyaran da ake bukata sai ya nuna kamar tun farko ba a rigaya an amince da kasafin kudin ba.(Fatimah Jibril)