Sanarwar da Farfesa Sambo Wali, shugaban majalissar bada shawara a kan al'amuran addini ya saka ma hannu ya ce wannan shawarar ta biyo bayan taron majalissar da aka yi a Sokoto.
Yayi bayanin cewa, ba su samu wata sanarwar ganin sabuwar watan Ramadan ba, abin ya nuna cewa, a yau Talata ya kasance 30 ga watan Sha'aban, Don haka Laraba za ta kama daya ga watan Ramadan na shekarar 1434 bayan Hijira.
Sanarwar har ila yau ta mika fatan alheri daga wajen Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar ga daukacin musulman kasar da za su fara azumi.(Fatimah Jibril)