Mista Wu Ping ya yi bayanin cewa, ta hanyar harba wannan kumbo, ana fatan cimma wasu burika 4, wato na farko, gwajin hada kumbon da wani kumbo na daban mai suna Tian Gong-1 dake shawagi a sama. Na biyu, ana son tabbatar da ganin cewa kumbon zai iya samar da muhalli mai dacewa, don 'yan jannati ta fuskar zamansu, da gudanar da ayyuka a cikinsa yadda ya kamata. Na uku, 'yan jannatin 3 za su gwada fasaharsu wajen sarrafa kumbo da gyaransa, tare da gudanar da sauran gwaje-gwaje. Na hudu, shi ne gwajin ingancin kumbon wajen shawagi bisa umarnin da aka ba su.
A cewar Mista Wu, kumbon Shen Zhou-10 zai yi kwanaki 15 yana shawagi a sama, sa'an nan a cikin wannan wa'adi zai hada jikinsa da kumbon Tian Gong-1 sau 2, daya bisa jagorancin na'ura mai kwakwalwa, dayan kuma bisa sarrafawar 'yan jannatin dake cikinsa. A yayin hadewar kumbon 2, 'yan jannatin za su shiga kumbon Tian Gong-1, inda za su gudanar da gwaje-gwaje. Daga bisani za su komo gida ta kumbon Shen Zhou-10. (Bello Wang)