Mark Lipdo, jami'in Stefanus Foundation, wata kungiya mai zaman kanta ya sheda ma kamfanin dillanci labarai na kasar Sin Xinhua cewa, mutane 33 ne aka kashe a sanyin safiyar ranar Alhamis a karamar hukumar Langtang dake jihar.
Shi ma shugaban rikon kwarya na karamar hukumar ta Langtang Narman Darko ya tabbatar da mutuwar wadannan mutane a kauyuka uku, abin da yake danganta shi da cewa, 'yan kungiyar ta'adda na Fulani ne suka aikata shi.
Kwamandan rundunar tsaro ta hadin gwiwwa a jihar Brigadier Janar Harry Ayoola shi ma ya tabbatar da mutuwar mutane da dama, amma ya ce, ba'a gama samun cikakken adadinsu ba sai dai jami'an tsaro tuni suka isa wurin, duk da suma sai da suka yi arangama da maharan kafin su samu nasarar wanzar da doka da oda, kuma ya zuwa yanzu sun kama wadansu da ake zargi da wannan hari da dama.(Fatimah Jibril)