in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An saki mutanen da aka yi garkuwa da su a Arewacin Mali
2013-07-22 10:00:41 cri
Mahukuntan kasar Mali sun tabbatar da sakin mutanen nan Biyar da wasu 'yan bindiga suka yi garkuwa da su, a garin Tessalit dake Arewacin kasar Mali kwana guda da sace su.

Mutanen 5 sun hada da mataimakin magajin garin na Tessalit, tare da ma'aikatan zabe su 4. Maharan da ake zaton magoya bayan kungiyar 'yan tawayen nan ta MNLA dake da alaka da Al-Qaida ne, sun saki mutanen ne a ranar Lahadi 21 ga wata ba tare da gindaya wani sharadi ba.

Wani jami'in hukuma dake Kidal, a lardin arewacin kasar mai fama da tashe-tashen hankula, ya ce jami'an tsaro sun samu nasarar cafke jagoran kungiyar ta MNLA, wanda ya ba da umurnin kame wadannan jami'ai.

A wani ci gaban kuma al'ummar wannan yanki na Kidal sun shiga halin firgici, bayan da jami'an tsaro suka gano wani abin fashewa da aka dasa a wata kasuwa a ranar Lahadi, koda yake dai an samu nasarar kwance wannan nakiya ba tare da ta tashi ba.

Wannan dai lamari na zuwa ne mako guda gabanin fara kada kuri'un babban zaben kasar dake tafe, a kuma lokacin da ake sake nazarin kan ko kasar ta Mali na iya gudanar da wannan zabe cikin nasara ko kuwa a'a, musamman ma a yankuna irin Kidal, wadanda ke karkashin ikon 'yan tawaye.

Idan dai za a iya tunawa cikin watan Janairun da ya gabata ne aka amince da tura sojojin kasar Faransa zuwa Mali, domin fatattakar magoya bayan kungiyoyin dake da alaka da Al-Qaida, wadanda ke kaka-gida a arewacin kasar kusan tsahon shekara guda. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China