Majiyar ta ce, an yi imanin cewa wasu kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayin jihadi da ke da alaka da magoya bayan hambararren shugaba Mohammed Morsi ne suka harbi jami'an tsaron guda 4 ciki har da guda 3 da suka kashe, yayin da na hudun da kuma farar hulan aka halaka su a wasu hare-haren da aka kai da makamai a kusa da wani ofishin 'yan sanda, hare-haren da majiyar ta ce aka ci gaba da kaiwa har zuwa wayewar garin ranar Litinin.
Bugu da kari a ranar Lahadi, maharan sun kai wani hari kan wani ofis da mashayar 'yan sanda da kuma wuraren duba ababen hawa na sojoji da ke biranen Arish da Rafah da ke zirin na Sinai.
Majiyar da ta bukaci Xinhua ta sakaye sunanta, ta bayyana cewa, mutane 17 din da suka ji mummunan rauni sun hada da jami'an tsaro 11 da fararen hula guda 6. Sama da mutane 25 ne aka kashe cikin makonni biyun da suka gabata, wadanda suka hada da sojoji, fararen hula a irin wadannan hare-haren da aka kai kan cibiyoyin tsaro da wuraren duba ababen hawa a arewacin Sinai.
Wadannan hare-haren sun sake kunno kai ne, bayan da sojoji suka goyi bayan boren da ya kai ga hambarar da Morsi a farkon wannan wata.
Bayanai na nuna cewa, rashin tsaro ne ya kara kazantar hare-haren da ake kaiwa da makamai kan cibiyoyin 'yan sanda, sojoji da wuraren duba ababen hawa a mashigin Sinai, bayan baron shekara ta 2011 da aka yi, wanda ya hambarar da tsohon shugaba Hosni Mubarak na Masar. (Ibrahim)