Gamayyar kungiyar SADC ce ta zabi kasar Afrika ta Kudu domin taimakawa jam'iyyun siyasa na kasar Zimbabwe warware badakalar siyasar dake tsakaninsu. Lindiwe Zulu, mamba na wannan kwamiti, kuma mashawarcin shugaba Zuma ta fuskar harkokin kasa da kasa, ya bayyana a ranar Jumma'ar da ta gabata cewa akwai kalubale kafin wadannan zabubuka, kuma halin da ake ciki a kasar Zimbabwe kafin wadannan zabubuka ba ya da kyau. Wadannan kalamai na mista Zulu sun harzaka shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe wanda nan take ya bukaci takwaransa Jacob Zuma da ya hana ma'aikacinsa yin katse landa kan harkokin cikin gida na kasar Zimbabwe. Furucin mista Lindiwe Zulu ba su dace ko kadan ba, kuma wasu kalaman nasa ba su da tushe, in ji mista Maharaj. Kuma wannan kwamiti ba ya da hurumin tilasta wa kasar Zimbabwe daukar ra'ayinsa ko yin wata sanarwa. Shugaban Zuma kadai ne aka baiwa wannan nauyi na yin magana kan kasar Zimbabwe da sunan kungiyar SADC. Hakazalika mista Maharaj ya karyata jita jitar da jaridu suka watsa dake nuna cewa shugaba Zuma ya kira shugaba Robert Mugabe ta wayar tarho a wannan mako domin bayyana masa rashin jin dadinsa kan yadda ake shirye-shiryen zabubuka a kasar Zimbabwe. (Maman Ada)