Kasar Sin ta mallaki tsibirin Diaoyu da sauran kanana tsibirai karkashin renonsa tun tuni. Kamata ya yi hukumar kula da yanayin saman kasar Sin da hukumar kula da tekun kasar Sin su dauki nauyin aikin bayar da hasashen yanayin wadannan wurare yadda ya kamata, domin yin rigakafin da kaucewa bala'u daga indallahi. Saboda aikin na da muhimmiyar ma'ana wajen ba da tabbaci ga ayyukan kama kifi da tsaron jiragen ruwa tare da kiyaye ikon mallakar teku na kasarmu baki daya.
Kafin wannan, ana ba da hasashen yanayi kawai ne kan muhallin yankin teku na tekun gabas na kasar Sin. (Maryam)