Jami'an kasar Sin da suka halarci taron sun ce, kasar Sin a shekarun baya ta gudanar da wasu bincike da gwaje-gwaje don dace da ra'ayin raya kasa tare da kiyaye muhalli, kana ta samu wasu fasahohin, wadanda suka sheda cewa, kafin a yada ra'ayin raya tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba, dale ne a yi kokarin kafa wani tsarin tattalin arziki mai inganci a duniya, gami da kafa wani tsarin da ake bi wajen gudanar da aikin kyautata muhallin duniya, wanda ya shaida daidaito, sanin ya kamata, da kuma inganci. Kana a yi kokarin sa kaimi ga kasashe masu sukuni da su kara tallafawa kasashe masu tasowa ta fuskar kudi da fasaha.
Taron an kaddamar da shi ne a ranar 21 ga wata, inda ministoci na kasashe sama da 140, da wakilan jama'a gami da manyan jami'ai a harkar kudi suke tattaunawa kan batun bunkasa tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba da kiyaye muhalli.
Taken taron shi ne bunkasa tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba, kuma ministocin kula da harkokin kiyaye muhalli na kasashe da dama za su tattauna da yin shawarwari, don rage da kawar da bambancin ra'ayi da ke akwai tsakaninsu wajen kiyaye muhalli. (Bello Wang)