Zhang ya ce, har zuwa yanzu kasar Sin ta kan fid da gurbatattun abubuwa da yawa zuwa muhalli, kana yayin da ake samun bunkasuwar tattalin arziki cikin sauri, wasu sabbin matsaloli ta fuskar muhalli su kan kunno kai. Daga cikinsu wadanda suka fi samarwa mutane wahalhalu sun hada da kayayyaki masu guba da ake samar daga masana'antu, da gurbatattun abubuwan da za su dore wajen lalata muhalli, gami da sharar kayayyakin lantarki, da dai makamantansu. Ban da haka kuma, an ce, kafin a daidaita matsalar gurbacewar ruwa da iska, an fara ganin yadda ake gurbata kasa a kasar.
Zhang Lijun, mataimakin ministan kiyaye muhallin kasar Sin, ya kara da cewa, kasar Sin tana kara saurin habaka birane da garuruwa, don haka a shekaru 5 masu zuwa za a kara samun wasu birane da garuruwa a kasar. Zuwa lokacin wasu manoma za su bar gidajensu dake karkara domin fara zama a birane, abin da ya sa ake bukatar kara samar da kayayyakin kiyaye muhalli a biranen kasar.
Haka zalika, Zhang ya bayyana cewa, a shekaru 5 masu zuwa, za a fi mai da hankali kan daidaita wasu matsaloli ta fuskar muhalli wadanda ke kawo cikas ga kokarin da ake yi don samun ci gaba mai dorewa, tare da kokarin warware wasu matsalolin muhalli da suka lalata lafiyar jama'ar kasar. (Bello Wang)