Wurare da yawa na fama da gurbacewar yanayi mai tsanani, dake janyo illa ga zaman rayuwar jama'ar Sin da ma lafiyar jikinsu.
Ran 14 ga wata, hukumar kula da harkokin kiyaye muhallin kasar ta Sin ya ba da wata sanarwa inda ta nuna cewa, a halin yanzu da jama'ar kasar suke fama da gurbacewar yanayi, kamata ya yi biranen kasar su mai da hankali kan ayyukan bincike ingancin iska yadda ya kamata.
Haka zalika sanarwar ta yi kira da a kara mai da hankali kan ayyukan kaucewar gurbacewar yanayi, da kuma dukufa wajen rage mugun tasirin da gurbacewar yanayi ta kawo wa jama'a, ta yadda za'a kiyaye lafiyar jama'ar kasar. Sanarwa ta kara da cewa, kamata ya yi a watsa labarai cikin lokaci kan ingancin iska ga al'ummomin kasar ta kafofin watsa labarai iri-iri, kamar su gidajen rediyo, shirye-shiryen talabijin, shafin intanet, da kuma jaridu da dai sauransu, ta yadda za a iya kiyaye ikon samar da bayanai kan yanayin muhalli ga jama'ar kasar.
Daga bisani kuma, hukumar kula da harkokin kiyaye muhallin kasar ta Sin ta bukaci a mai da hankali kan kananan abubuwa cikin iska dake gurbata muhalli, da kuma dukufa kan ayyukan kiyaye muhalli yadda ya kamata. (Maryam)